logo

HAUSA

Ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar da rahoton shekara-shekara kan karfin sojan Sin da nufin fakewa wajen nuna danniya ko babakere a fannin soja

2022-11-30 19:40:58 CMG Hausa

Dangane da rahoton shekara-shekara da ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar kan karfin sojan kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Laraba 30 ga wata cewa, a cikin 'yan shekarun nan, Amurka ta yi ta yayata nau'o'i daban-daban na "Ra’ayin barazanar da Sin ke kawowa", da nufin neman fakewa don fadada makaman nukiliyarta, da kuma ci gaba da nuna danniya ko babakere a fannin aikin soja. Wannan dabara ce gama-gari ta Amurka, kuma duk duniya na sane da hakan.

Kakakin ya kara da cewa, a matsayinta na kasa mafi girma da ke da makaman nukiliya, Amurka ta ci gaba da inganta karfinta a fannin a cikin 'yan shekarun nan, tare da ci gaba da karfafa rawar da makaman nukiliya ke takawa a manufofinta na tsaron kasa. Ta kuma yi tsayin daka wajen bin manufar amfani da makaman nukiliya don kawo barazana ga saura, har ma a fili ta na daidaita dabarun musamman na amfani da makaman nukiliya don yin barazana ga wasu kasashen na musamman, har ma tana yin hadin gwiwa da Birtaniya, da Autiraliya kan jirgin karkashin ruwa dake aiki da karfin nukiliya da ke saba wa buri da manufar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)