logo

HAUSA

Li Keqiang ya gana da takwaransa na Kazakhstan

2022-11-30 11:31:18 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwaransa na kasar Kazakhstan Álihan Ashanuly Smaıylov ta kafar bidiyo a babban dakin taron jama'a da yammacin ranar jiya Talata.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana fatansa na inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Kazakhstan zuwa wani sabon mataki, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban yankin da kasashen 2 ke ciki. Li ya kara da cewa, Sin da Kazakhstan makwabta ne kwarai, kuma tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekaru 30 da suka gabata, dangantakar bangarorin biyu ta sami ci gaba mai ma’ana, wadda ta kawo alheri ga kasashen biyu da al’ummunsu. A watan Satumban bana, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ziyarci Kazakhstan cikin nasara, wadda ta kara azama kan samun sabon ci gaba wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Bangaren Sin yana fatan yin mu’ammala da kasar Kazakhstan, wajen kara yin mu’ammala tsakanin manyan jami’ai tuntubar juna a matakai daban daban, da kyautata taimakawa juna a fannin raya kasa bisa manyan tsare-tsare, da inganta hadin gwiwa a sassa daban daban, da kara taimakawa jua a harkokin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, da daga matsayin dangantakar Sin da Kazakhstan zuwa wani sabon mataki, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban yankin da kasashen 2 ke ciki.

A nasa bangare, Smaıylov ya ce, bangaren Kazakhstan ya dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninsa da Sin, yana fatan amfani da bikin cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya da Sin a matsayin wata dama ta zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa a tsakaninsa da bangaren Sin, ta aiwatar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da karfafa mu’ammala da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da makamashi da aikin gona da kara mu’ammala tsakanin al’umma, da inganta huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Kazakhstan da Sin.(Safiyah Ma)