logo

HAUSA

Sanarwar kwamitin jana'izar Jiang Zemin

2022-11-30 20:49:39 CMG Hausa

Domin bayyana girmamawa da jajantawa daga dukkan jam'iyyar JKS, sojoji da al'ummomin kasa baki daya ga marigayi Jiang Zemin, an yanke shawarar yin haka,

Da farko, tun daga ranar da aka fitar da wasika zuwa ga daukacin jam’iyyar da sojoji da al’ummar kasar Sin, har zuwa ranar taron tunawa da Jiang Zemin, filin Tiananmen, da Xinhuamen, da babban dakin taron jama'a, da ma'aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin mu’amala na gwamnatin tsakiya dake yankin musamman na Hong Kong, da ofishin mu’amala na gwamnatin tsakiya dake yankin musamman na Macau, da ofisoshin jakadancin kasar Sin, da kananan ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen waje za su sassato tutar kasa-kasa.

A cikin wannan lokaci, ofishin mu’amala na gwamnatin tsakiya dake yankin musamman na Hong Kong, da ofishin mu’amala na gwamnatin tsakiya dake yankin musamman na Macau, da ofisoshin jakadancin kasar Sin da kananan ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen waje, sun kafa wuraren zaman makoki, domin karbar ta'aziyya daga Hong Kong, Macao da kasashen da suka karbi bakuncinsu.

Na biyu, bisa al’adar kasar Sin, ba za a gayyaci gwamnatoci, jam'iyyun siyasa da abokan kasashen waje, su aika tawaga ko wakilai zuwa kasar Sin domin halartar ayyukan zaman makoki ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)