logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin ya yaba wa takadar ba da shawara ta Tianjin

2022-11-30 13:49:32 CMG Hausa

Ana gudanar da babban taron bitar yarjejeniyar hana makaman halitta karo na 9 a babban ginin MDD dake birnin Geneva na kasar Switzerland. A jiya Talata, jami’ar Tianjin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin sun shirya wani taron hadin gwiwa kan takardar ba da shawara ta Tianjin dangane da ka’idojin da masana kimiyya suke bi a harkokin tsaro masu nasaba da illolin da nazarin halittu ke haifarwa dan Adam da muhalli, wato Tianjin Guidelines a Turance.

Shugaban tawagar Sin dake halartar babban taron kuma jakadan kasar mai kula da harkokin kwance damara, Li Song, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, masana kimiyya daga kasashe fiye da 20 ciki har da kasar Sin, sun fito da takardar ta Tianjin ga al’ummomin duniya, wadda ta dace da yanayin da muke ciki, kuma ta bayyana yadda masana kimiyya daga kasashe daban daban suke inganta hadin gwiwarsu a harkokin tsaro masu nasaba da illolin da nazarin halittu ke haifarwa dan Adam da muhalli, yayin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Jami’in hukumar goyon bayan aiwatar ta yarjejeniyar hana makaman halitta, ya bayyana cewa, takardar ta Tianjin, ta kasance a matsayin abin koyi ga masana kimiyya na duniya a fannin inganta rawar da yarjejeniyar hana makaman halitta take takawa. An riga an yi tattaunawa kan takardar an kuma amince da ita sosai.  

Haka zalika, wakilai daga kasashen Pakistan da Brazil, da Rasha, da Philippines da Cuba da sauran kasashe, sun bayyana goyon bayansu ga “Tianjin Guidelines”, sun kuma yaba da rawar da kasar Sin take takawa. Haka kuma sun yi kira ga babban taron bitar yarjejeniyar hana makaman halitta karo na 9, da ya mayar da “Tianjin Guidelines” a matsayin muhimmin sakamakon taron.(Safiyah Ma)