logo

HAUSA

Senegal ta samu damar kaiwa ga zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya na Qatar

2022-11-30 11:12:20 CMG Hausa

A jiya ne, kasar Senegal ta yi nasarar doke Ecuador, a gasar cin kofin duniya dake gudana yanzu haka a kasar Qatar. ’Yan wasan Senegal Isma’ila Sarr da Kalidou Koulibaly ne suka jefawa kasarsu kwallaye a ragar Ecuador, kuma karon farko cikin shekaru 20 da kasar ta samu damar kaiwa mataki na kifuwa daya kwale na gasar. An dai tashi wasan na jiya ne, ci biyu da 1. (Ibrahim)