logo

HAUSA

Jiang Zemin ya rasu

2022-11-30 18:20:10 CMG Hausa

Jiang Zemin ya rasu da tsakar ranar yau Laraba da karfe 12:13 a birnin Shanghai, yana da shekaru 96 a duniya. Rahotanni sun ce kafin rasuwarsa ya sha fama da sankarar jini da mutuwar wasu sassan jiki.

Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS), da zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, da majalissar gudanarwar kasar, da kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, da hukumar kolin rundunar sojoji ta JKS da janhuriyar jama’ar kasar Sin suka tabbatar da hakan.

Sassan sun fitar da sanarwar hakan ne cikin wata wasika da aka aike ga ilahirin JKS, da rundunar sojojin kasar, da kuma daukacin Sinawa daga dukkanin kabilu.

Wasikar ta bayyana Jiang Zemin a matsayin jajirtaccen shugaba mai martaba, wanda dukkanin ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin suka aminta da shi, wanda ya samu karbuwa daga rundunar sojojin kasar Sin, da daukacin al’ummar Sinawa, kana babban mabiyin akidar Markisanci, kuma babban masani a fannin siyasa da ayyukan soji da diflomasiyya, kuma jarumin jam’iyyar kwaminis da ya taka rawar gani, kuma shugaba na gari a tafarkin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin. Kaza lika marigayin jigo ne na jagororin kasar Sin na zuriya ta uku, wanda ya kafa ginshikin ka’idar mulki ta “wakilci a fannoni uku”.  (Saminu Alhassan)