logo

HAUSA

Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka

2022-11-30 19:04:54 CMG Hausa

Wani batu dake kara janyo hankalin duniya shi ne, matsalar sauyin yanayi. Abin da ya sa MDD ta shirya taruka a lokuta daban-daban, da nufin ganin an kawar da wannan matsala dake kokarin gagarar kwandila. Guda daga cikinsu shi ne taron COP27, na sassa da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, da aka kammala a Masar ba da dadewa ba.

A karshen wannan taro, an cimma matsayar kafa wani asusun musamman da nufin agazawa kasashen da wannan matsala da fi shafa. Baya ga kasancewar taron wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci. Duk da cewa, kudaden da ake fatan tarawa ba za su isa ba, yunkurin tara kudaden kadai, tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce.

Nahiyar Afirka na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi karancin sinadarai, da iska mai gurbata muhalli a duniya, amma a hannu guda, nahiyar na sahun gaba wajen dandana kuda daga mummunan tasirin sauyin yanayi. Masu fashin baki na ganin duba da yadda kasar Sin ke kan gaba, wajen cin gajiya daga fasahohin dakile sauyin yanayi, musamman fannin bunkasa amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbata muhalli, da wadanda ake iya sabuntawa. Kuma kasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga kasashen Afirka a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci ya yi da kasashen na Afirka za su fadada koyi daga kasar Sin a wannan fanni. Ko shakka babu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin kasashen nahiyar Afirka na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a daya bangaren kasar Sin ke da kwarewa, da fasahohin bunkasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi hadin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.

Wadannan hujjoji, na kara nuna muhimmancin aza kyakkyawan harsashi, na ingiza hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kare muhalli, da bunkasa cin gajiya daga nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa. Kana idan har mafarkin kafa wannan asusu ya tabbata tare da aiwatar da shi kamar yadda aka tsara, da ma sauran matakai da tsare-tsare da hadin gwiwar kasashe da cika alkawuran da aka dauka to, babu tantama watan-wata rana batun matsalar sauyin yanayi za ta kasance tarihi.(Ibrahim Yaya)