logo

HAUSA

Shugaba Xi ya sha alwashin karfafa hadin gwiwar kasarsa da Rasha a fannin makamashi

2022-11-29 20:40:22 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasar sa a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Rasha a fannin makamashi. Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, cikin sakon da ya aike ga taron cinikayyar makamashi na Sin da Rasha karo na 4, ya ce hadin gwiwa a fannin makamashi muhimmin jigo ne na hadin gwiwar sassan 2, kuma muhimmin karfi dake iya tabbatar da isasshen makamashi a duniya.

Cikin wasikar tasa, shugaban na Sin ya kara da cewa, yayin da ake fuskantar hadurra da kalubale daga sassan waje, Sin da Rasha sun karfafa tuntubar juna, tare da ingiza ayyukan hadin gwiwa, wanda hakan ke nuni ga juriyar da hadin gwiwar su ke da ita a fannin makamashi, da ma sauran manyan abubuwan da suka sanya gaba cikin hadin gwiwarsu, bisa manyan tsare-tsare a sabon karni.  (Saminu Alhassan)