logo

HAUSA

Lai Mohammed: Najeriya na cin gajiya daga hadin-gwiwar ta da kasar Sin

2022-11-29 14:57:33 CMG Hausa

Lai Mohammed, shi ne ministan watsa labarai da al’adu na tarayyar Najeriya. A yayin da yake zantawa da manema labarai kwanan nan a Abuja, hedikwatar kasar, ya yi tsokaci kan hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasarsa da kasar Sin, inda a cewarsa, hadin-gwiwa da mu’amalar kasashen biyu, na da makoma mai haske.

Lai Mohammed ya ce, kasar Sin ta samu dimbin nasarori a fannin inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da sauran fannonin da suka shafi kawar da talauci, da bunkasa kimiyya da fasaha da harhada magunguna da makamantansu. Yana mai cewa:

“Ina farin cikin ganin cewa, a matsayin wata kasa dake tasowa, Najeriya ta ci alfanu daga ci gaban kasar Sin, saboda akwai hadin-gwiwa da mu’amala sosai tsakanin kasashen biyu. Sanin kowa ne, inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, jigo ne na ci gaban kasa. Kuma ana iya ganin cewa, Najeriya ta zuba makudan kudade a wannan fanni, ciki har da zamanantar da tsarin layukan dogo, da shimfida hanyoyin mota na zamani, da gina manyan gadoji, da kuma sake raya filayen saukar jiragen sama da sauransu. Abun farin-ciki shi ne, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a wadannan fannoni, saboda akwai kamfanonin China da yawa da suke gudanar da ayyukan inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a Najeriya. Akwai alaka ta kut da kut tsakanin kasashen biyu.”

Ministan ya kuma jaddada cewa, gwamnatin Najeriya tana nuna himma da kwazo wajen aiwatar da shirye-shirye na tallafawa al’umma, ciki har da shirin bada kudade na kai-tsaye na taimakawa mutanen dake zama a yankunan karkara, da shirin raya sana’ar samar da ababen hawa da sauransu, wadanda ke taimakawa al’umma kawar da talauci, tare da samar musu da guraban ayyukan yi.

A watan Oktobar bana, an yi babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a Beijing, wanda ba wani muhimmin al’amari ne ga al’ummar kasar kadai ba, har ma ya bayyana muhimman dalilan da suka sa kasar ta iya samun ci gaba a baya, da manufofin kasar na samar da ci gaba a nan gaba, wadanda sauran kasashe za su iya cin moriya, ko kuma koyon darasi daga ciki. Lai Mohammed ya bayyana cewa:

“Na farko, bari in yi amfani da wannan dama don taya gwamnatin kasar Sin murna, saboda cimma nasarar gudanar da wannan babban taro na wakilan jam’iyyar kwaminis a Beijing, al’amarin da ya shaida cewa, jam’iyyar kwaminis mai mulkin China, tana gudanar da harkokin mulki bisa daidaito. A gani na, hakan zai taimaka sosai ga kara ci gaban kasar Sin zuwa gaba, da samar da alfanu ga daukacin al’ummar ta.”

Ministan ya kara da cewa, duniya ma tana cin gajiya sosai daga dimbin nasarori da ci gaban da kasar Sin ta samu, musamman bisa muhimmiyar shawarar nan da ake kira “Belt and Road” initiative, ko kuma shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A shekara ta 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bullo da muhimmiyar shawarar “ziri daya da hanya daya”, a kokarin karfafa hadin-gwiwa tare da kasashe daban-daban, bisa tafarkin zaman lafiya da adalci, a fannonin da suka shafi tattalin arziki da kasuwanci da sauransu, domin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Ya zuwa karshen shekara ta 2021, daga cikin kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diflomasiyya tare da kasar Sin, akwai guda 52, gami da kungiyar tarayyar Afirka AU, wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin-gwiwa tare da kasar Sin domin aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, abun dake taimakawa sosai ga inganta hadin-gwiwar bangarorin biyu a fannonin tattalin arziki da kasuwanci da sauran su.

Lai Mohammed ya yi fashin baki kan muhimmancin wannan shawara, inda ya ce:

“Shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ na taimakawa sosai wajen samar da guraban ayyukan yi, da inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a sassa da dama na duniya. Muna iya cewa, kasar Sin dake karkashin mulkin jam’iyyar kwaminis, tana bada babbar gudummawa ga ci gaban duk duniya.”

A matsayin sa na babban jami’in dake kula da harkokin watsa labarai da al’adu na tarayyar Najeriya, Lai Mohammed ya kuma ce, yana farin-ciki sosai da ganin ingantar hadin-gwiwa da mu’amala tsakanin kafafen yada labaran kasashen Najeriya da China, musamman a wani sabon shirin talabijin dake kunshe da bayanai da yawa da ake kira “Sabuwar Tafiyar Kasar Sin”, ko kuma “China: A New Journey”. Ya ce, an dade da karfafa gwiwar kasashen biyu a fannin daukar shirye-shiryen talabijin da fina-finai tare. Ga abun da yake cewa:

“Sanin kowa ne, masana’antar fina-finai da shirye-shiryen talabijin ta Najeriya tana kan gaba a nahiyar Afirka. Ina maraba da duk wani hadin-gwiwa tsakanin Najeriya da sauran kasashe a fannin daukar fina-finai ko shirye-shiryen talabijin. Ban taba ganin wannan shirin talabijin ba, amma na ji an ce akwai abubuwa da yawa a ciki, dake bayyana yadda ake noman sabbin nau’o’in shinkafa, wadanda za su girma da samun yabanya mai armashi a Najeriya. Irin wannan abu zai samar da alfanu ga manoman kasar mu, da kara musu ilimi a fannin aikin gona. Za’a kara samun yabanyar shinkafa mai armashi, idan aka kwatanta da aikin gonar mu na gargajiya. Ina matukar sha’awar ganin wannan shirin talabijin, kuma ina yabawa hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kafafen yada labaran kasashen Najeriya da China, wato gidan talabijin na kasa na NTA da China Media Group CMG, wato babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin. Ina kuma fatan wannan zai bude mana sabon babi, wajen fadada hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin daukar shirye-shiryen talabijin da fina-finai.” (Murtala Zhang)