logo

HAUSA

Shugaban CMG ya gana ga shugabar AP ta kafar bidiyo

2022-11-29 18:59:25 CMG Hausa

Yau Talata 29 ga wata, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar, Shen Haixiong, ya gana da shugabar kamfanin dillancin labaran Associated Press na Amurka wato AP, Daisy Veerasingham ta kafar bidiyo, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra’ayi, tare da tattaunawa kan batutuwan da suka hada da alhakin kafafen watsa labaru, sadarwar hadin gwiwa, da ci gaban kafofin yada labaru da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)