logo

HAUSA

Serbia da Kamaru sun ci gaba da nuna fatan fafatawa a gasar cin kofin duniya na Qatar

2022-11-29 10:47:57 CMG Hausa

Kungiyoyin wasa na kasashen Serbia da Kamaru, sun fuskanci matsin lamba, wajen farke kwallayen da aka zura musu a fafatawar rukuni na G jiya Litinin, inda suka ci gaba da nuna fatan shiga zagayen kasashe 16 da za su fafata a zagayen gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar.

Jean-Charles Castelletto ne ya fara zura kwallo a ragar Serbia, a mituna na 29 da fara wasa, abin da ya baiwa kasarsa kwallon farko, a bugun kusurwa daga bangaren hagu da suka samu.

Serbia ta sauya wasan, bayan kwallaye biyun da ta zura a ragar Kamaru a cikin karin lokaci kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai cikin mituna 8 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Aleksandar Mitrovic, ya jefa kwallo ta uku a ragar kamaru, inda wasa ya zama ci 3 da 1.

Kamaru, wadda ke neman nasara ta farko a gasar, tun shekarar 2002, ta matsa kaimi, inda Vincent Aboubakar ya jefa kwallo ta biyu a ragar Serbia a mituna na 63, daga bisani kuma Choupo-Moting ya zura tasa kwallon bayan mintuna uku.(Ibrahim)