logo

HAUSA

Kasashen Sin da Mongoliya suna hada hannu don inganta zamanintarwa a sabon zamani

2022-11-29 21:46:38 CMG Hausa

A yammacin jiya Litinin 28 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Mongoliya Ukhnaagiin Khurelsukh wanda yake ziyarar aiki a kasar Sin, inda bangarorin biyu suka amince da hada karfi domin inganta zamanintarwa, tare da cimma matsaya mai mahimmanci wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma tsakanin kasashen biyu a sabon zamani.

Ukhnaagiin Khurelsukh, yana daya daga cikin shugabannin muhimman kasashe makwabta da kasar Sin ta karbi bakuncin su, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, kuma wannan ne karo na farko da ya kai ziyara kasar Sin, bayan ya dare kujerar shugaban kasar Mongoliya.

A cewar sanarwar hadin gwiwa da kasashen biyu suka fitar, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa guda 16, inda suka amince da mayar da yin cudanya, da makamashi, a matsayin daya daga cikin muhimman batutuwan hadin gwiwa.

A matsayinsu na makwabta kuma abokai, Sin da Mongoliya na ci gaba kafada da juna kan hanyar zamanintarwa, ko shakka babu za su samu ci gaba da wadata tare a sabon zamani. (Mai fassara: Bilkisu Xin)