logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya jinjinawa ‘yan wasan Black Stars kan yadda suka doke Koriya ta kudu

2022-11-29 09:24:31 CMG Hausa

Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana, ya taya tawagar Black Stars ta kasar murnar doke Koriya ta kudu a gasar wasan cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a Qatar.

Akufo-Addo ya fada a shafinsa na Tiwita cewa, ‘yan wasan sun cancanci wannan nasara. Yana mai cewa, “Ina yabawa ‘yan wasan Black Stars. An barje gumi, amma kun cancaci nasarar da kuka yi a kan Koriya ta kudu. Ina alfahari da baki dayan tawagar da ma goyon bayan da al’ummar Ghana suka ba su”.

Shugaban ya kuma bukaci kungiyar, da ta mayar da hankali kan wasan karshe na rukinin H da za su fafata da Uruguay ranar Jumma’a. Yana mai cewa, “Za mu yi nasara”.

Mohammed Kudus ne, ya zura kwallaye biyu da ya baiwa Ghana nasara a wasan da suka doke Koriya ta kudu jiya Litinin da ci 3 da 2. (Ibrahim)