logo

HAUSA

Sin ta harba kumbon Shenzhou-15 dauke da ‘yan sama jannati 3

2022-11-29 23:53:06 CMG Hausa

A daren yau Talata ne kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Shenzhou-15 ta amfani da rokar Long March 2F Y-15. Shenzhou-15 ya shiga sararin samaniya dauke da‘yan sama jannati su 3, bayan harba shi daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. (Saminu Alhassan)