logo

HAUSA

Yan sama jannati uku na kasar Sin za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15

2022-11-28 10:03:29 CMG Hausa

Ofishin kula da aikin binciken sararin samaniya na kumbo mai dauke da 'yan sama jannati na kasar Sin ya bayyana cewa, ofishin ba da umurni na ayyukan kumbon binciken sararin samaniya na kasar Sin, ya tsaida kuduri cewa, 'yan jannati uku wato Fei Junlong, da Deng Qingming, da Zhang Lu za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15, karkashin jagorancin Fei Junlong.

Gobe Talata ne, za a harba kumbon Shenzhou-15 cikin sararin samaniya daga cibiyar harbar kumbona ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. (Zainab)