logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da sabon jakadan Rasha dake kasar Sin

2022-11-28 10:26:42 CMG Hausa

Ministan wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da sabon jakadan Rasha dake kasar Sin Igor Morgulov jiya Lahadi, inda mista Wang ya ce, duk da yadda yanayin duniya yake sauyawa, a matsayinsu na makwabta, Sin da Rasha za su inganta amincewar juna bisa manyan tsare-tsare da handin gwiwa mai amfani, da karfafa abokantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kokarin tabbatar da adalci a duniya tare.

Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Rasha dukkansu na tsayawa tsayin daka kan manufar girmama ra’ayoyin bangarori daban daban yayin da ake lura da harkokin kasa da kasa, suna kuma adawa da ra’ayi na samun wani bangare daya tak dake yin babakere a duniya. Sin da Rasha za su nace ga kokarin kare tsarin duniya wanda MDD ke zama jagora da gudanar da harkoki bisa dokokin kasa da kasa, da adawa da tsarin siyasa na nuna karfin tuwo. Wannan matsayi an tabbatar da shi ne bisa tantance abubuwan da suka faru a baya, kuma ya dace da yanayin ci gaban zamani.

A jawabinsa, jakada Igor Morgulov ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin tana da inganci kuma babu wanda zai iya lalata ta ba, haka kuma ta hanyar dogaro kan wannan abokantaka ana iya warware dukkan kalubalolin da za a fuskanta. Ya ce, bangaren Rasha na son ganin ci gaban Sin, yana kuma fatan inganta dangantakarsu ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon matsayi.(Safiyah Ma)