logo

HAUSA

Shugaban majalisar zartaswar Turai zai ziyarci kasar Sin

2022-11-28 19:21:34 CMG Hausa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai Charles Michel, zai ziyarci kasar Sin a ranar 1 ga watan Disamba dake tafe.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta tabbatar da hakan a yau Litinin. (Saminu Alhassan)