Shirin Spring Bud ya kyautata rayuwar ‘yan matan Tibet
2022-11-28 10:28:26 CMG Hausa
A shekarar 1989, asusun kula da yara da matasa na kasar Sin ya kaddamar da wani shiri mai suna Spring Bud, domin taimakawa yaran da suka fito daga gidaje matalauta, komawa makaranta da inganta ilimin ‘ya’ya mata a yankunan dake fama da talauci.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, cikin shekaru 10 da suka gabata, shirin ya tallafawa ‘yan mata miliyan 1.76, kuma ya samar da hidimar taimakawa yaran kai tsaye, ta hanyar ba da shawarwari ga ‘yan mata 133,400. Bayan samun tallafi daga shirin, ‘yan matan ba sa mantawa da sakawa al’umma. Ta hanyar bayar da kulawa da kauna ta hanyoyi daban-daban, ‘yan matan sun nuna ruhin shirin Spring Bud, ta hanyar samun ci gaba da jajircewa da hazaka da kyautata rayuwarsu.
A cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku labarin ‘yan matan da suka amfana da shirin, suke kuma bayar da gudummuwa da kuma karfafawa al’umma gwiwar raya ilimin ‘ya’ya mata. Sonam, daya ce daga cikinsu.
“Na yi matukar sa’a, shirin Spring Bud ya ba ni damar yin rayuwa ta daban,” abun da Sonam, wadda a baya iyayenta suka kasance matalauta a kauyen Sa’gya, wata gunduma a lardin Tibet mai cin gashin kansa dake kudu maso yammacin kasar Sin, ke yawaita fadi ke nan.
A lokacin da take da shekaru 6, Sonam ta kasance ‘ya mace ta farko da ta shiga makarantar firamare. Bayan ta kammala jami’a a 2011, ta zama mace ta farko mai mukamin hafsa a rundunar sojin kasar Sin (PLA), da ta fito daga kauyen Sa’gya.
Cikin shekaru 11 da suka gabata, Sonam ta kaunaci aikinta a rundunar sojin. Haka kuma tana shiga ana damawa da ita sosai, cikin ayyuka daban daban wadanda suka dace da karfafa hadin kai tsakanin rundunar da al’umma. Tana iyakar kokarin wajen ganin ta bada gudummuwa ga al’umma.
Yayin wani taron karawa juna sani da aka yi a baya-bayan nan, Sonam ta gabatar da kanta kamar haka, “sunana Sonam, hafsa mace a rundunar PLA, ‘yar kabilar Tibet, wadda ta taso da dimbin taimakon asusun CCTF da rundunar sojin sama ta PLA, karkashin shirin Spring Bud, da kuma tallafin kungiyar mata ta kasar Sin da kungiyar mata ta lardin Tibet.” Ta kara da cewa, ba za ta taba mantawa da tallafin da ta samu ba, domin ya sauya rayuwarta.
Iyayen Sonam, makiyaya, sun haife ta ne a shekarar 1988. Ta kan tuna mafarkinta na fita daga yankin tsaunika domin zuwa makaranta, wanda ba ta tsammaci cikarsa.
An fara aiwatar da shirin Spring Bud ne a Tibet a shekarar 1994. A lokacin, ba a fara aiwatar da tsarin tilasta karatu na tsawon shekaru 9 a Tibet ba, kuma babu wani mazaunin kauyensu da ya taba zuwa makaranta.
A shekarar 1994, Spring Bud ya kafa makarantar firamare ga ‘ya’ya mata a Sa’gya. Bayan jin labarin makarantar, sai iyayen Sonam suka tambaye ta ko tana son zuwa. Duk da ba ta san me ake yi a makaranta ba, nan take ta amsa da “Eh”, saboda ta zaku ta ga wani wuri na daban da ba kauyensu ba. An sanya Sonam a makaranta, inda ta kasance daya daga cikin dalibai 50 na ajin. Bayan shekara guda, sai ajin ya fara samun tallafin kudi daga rundunar sojin sama ta PLA, sannan kuma ya shiga karkashin shirin Spring Bud. Har yanzu Sonam kan tuna tufafinta na makaranta mai kyan gani, kuma babu bukatar iyayenta su biya kudin makaranta ko sayen kayayyakin karatu.
A cewar Sonam, ita da sauran daliban ajin, sun taso da kauna da kulawa daga kungiyar mata ta kasar Sin da rundunar sojin saman kasar. Ta ce tana matukar alfahari da damar da ta samu, don haka ta dage wajen karatu.
Bayan shekaru 6, Sonam ta zama daliba daya tilo da ta bar Sa’gya ta shiga makarantar Midil ta Jinan na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin, wanda aka ware ga yaran lardin Tibet.
Bayan shekaru 3, Sonam ta shiga babbar sakandare, kuma bayan ta kammala, ta fara karatu a jami’ar nazarin harkokin kasuwanci da tattalin arziki ta kasa da kasa(UIBE) dake Beijing.
Sonam ta ce, “da babu shirin Spring Bud, kila da ina kiwon Shanu a cikin tsaunika kamar sauran mutanen kauyenmu, kuma ba zan samu damar karatu a muhimmiyar jami’a ba.”
Yayin da take shekarar karshe a jami’a, Sonam ta ci jarrabawar neman aikin gwamnati. Amma daga baya, ba ta karbi aikin da aka ba ta ba, maimakon hakan, sai ta shiga rundunar sojin saman kasar Sin, karkashin wani shiri da aka ware ga tsoffin daliban Spring Bud.
Sonam na daya daga cikin dalibai 5, daga daliban Tibet, da suka shiga rundunar a shekarar 2011. Ta cika da farin ciki da kuma fargaba, a lokaci na farko da ta sanya kakin soji. Nan da nan labarin shigarta aikin soji, ya karade kauyen. Iyayenta sun yi farin ciki tare da alfahari da ita.
Tun bayan shigarta aikin soji, Sonam ta kasance mai kula da kyautata dangantaka tsakanin al’umma da rundunar sojin, da batutuwan tsaro da sauran harkokin mulki. Ta samu yabo sosai daga shugabanninta da ma sauran abokan aikinta.
Baya ga haka, Sonam ta taka rawa sosai a matsayinta na ‘yar kabilar Tibet, musamman yayin da take shiryawa da shiga shirye-shiryen da aka tsara domin inganta mu’amala tsakanin rundunar PLA da kananan hukumomi da al’ummomi.
A shekarun baya-bayan nan, rundanar su Sonam, ta bayar da gudunmuwar kudi wajen gina makarantun firamare 9 karkashin shirin Spring Bud da kuma makarantar rainon yara 1, a Tibet. Sonam ta kasance tamkar wata gada, ta fuskar shirye-shiryen da suka shafi ziyarce-ziyarce da bayar da gudunmuwa.
Har ila yau, tun daga 2012, ake damawa da ita kai tsaye, a shirye-shiryen yaki da talauci a kauyuka 7 na Tibet, a lokacin da rundunarta ta aiwatar da wasu shirye-shiryen bayar da tallafi.
Sonam ta kan ce tana farin ciki da ganin mutane, kamar iyayenta na samun tallafi daga rundunar sojin sama ta PLA. Tana da burin fadada bayar da tallafin ga mutane mafi bukata a shekaru masu zuwa.
Saboda jinjinawa kokarinta, rundunar sojin PLA, ta ba ta lambar yabo na aji na 3, haka kuma ta samu lambar yabo ta mata mafiya nagarta da kungiyar mata ta Tibet ta bayar, da kuma karramawa a matsayin abar koyi wajen hada kan ‘ya’yan kabilar Tibet. Kana gwamnatin lardin Tibet, ta ba rundunarsu Sonam lambar yabo dangane da kokarinsu na yaki da talauci a yankin a shekarar 2019.
A cewar Sonam, shirin Spring Bud ya samarwa dubban ‘yan mata kamar ta, dimbin damarmakin ci gaba da neman ilimi, da girma cikin koshin lafiya da rayuwa mai kyakkyawar makoma.
Saboda samun kwarin gwiwa daga labarin Sonam da sauran ‘yan matan da suka samu tallafin Spring Bud, iyalai da dama sun sanya ‘ya’yansu a makaranta, tare da ba su goyon baya a kokarinsu na kyautata rayuwarsu a wajen kauyukansu.
Galibin ‘yan ajin su Sonam, sun samu aikin gwamnati, wasu sun zama malamai, wasu likitoci, kuma dukkansu suna jajircewa kan ayyukansu.
Bugu da kari, Sonam da abokan karatun nata, suna shirin kaddamar da wata tawaga ta musammam, ta kyautata mu’amala tsakanin rundunar soji da bangarorin fararen hula.
Za su yi aikin sa kai a matsayin malamai a kauyuka masu nisa, inda za su rika bayani game da dabarun JKS da kuma dabarun kiwon lafiya da na tsaron kasa da dokoki, ga dalibai da iyayensu. (Kande Gao)