logo

HAUSA

Yankin Tigray na Habasha ya karbi tallafin farko bayan yarjejeniyar zaman lafiya

2022-11-28 10:10:20 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa, sama da mutane 450,000 dake zaune a yankin arewacin Tigray na kasar da ke fama da rikici ne a karon farko suka samu taimakon jin kai, tun bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanyawa hannu a kwanan nan.

Jami'an hukumar kula da bala'i ta kasar Habasha (NDRMC) sun bayyana a yammacin ranar Asabar cewa, gwamnatin kasar Habasha ta kara kaimi wajen samar da agaji ga masu rauni a yankin Tigray, ta hanyoyin mota guda 4 da na jiragen sama.

A cewar hukumar, a zagayen farko na kayayyakin jin kai kadai, an raba sama da kilogram dubu 90 na alkama da abinci mai gina jiki ga mutane sama da 450,000.

Hukumar ba da agaji ta kasa ta kara da cewa, sama da manyan motoci 60 makare da kayayyakin jin kai, sun isa wuraren da aka shirya za su je a yankin.

Batun agajin jin kai na baya-bayan nan a yankin Tigray, na zuwa ne bayan manyan kwamandojin gwamnatin Habasha da 'yan tawayen Tigray (TPLF), dake iko da yankin Tigray, sun amince da samar da agajin jin kai a sassan arewacin Habasha da ke fama da rikici a wata yarjejeniya da kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta shiga tsakani.(Ibrahim)