logo

HAUSA

Matasan Sin masu fasaha sun lashe lambobin yabo bakwai a gasar duniya

2022-11-28 11:42:57 CMG Hausa

A yayin bikin ba da lambar yabo da ya gudana jiya a Austria, matasan da suka fafata a gasar fasaha ta musamman ta duniya ta 2022 daga kasar Sin, wato Zhu Ke, Jiang Xinhua, Jiang Yuhe, Wu Yuanzhou, Yu Shouan da Jiang Hao sun sami lambobin zinare na nau'ikan jigilar hajoji, da bangaren fasahar manyan motoci, da fasahar dakin gwaje-gwajen sinadarai, da yin bulo, da hada na'urorin lantarki da kula da masana'antu, bi da bi.

Masu fasaha na kasar Sin da suka hada da Zhang Yangguang da Liu Jinyao, sun samu lambar tagulla a fannin aikin gine-gine.

Jiang Yuhe ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua bayan bikin cewa, ta yi farin ciki da alfahari da samun lambar zinare ta farko ta fasahar dakin gwaje-gwajen sinadarai da kasar Sin ta lashe a gasar fasaha ta duniya, inda ta bayyana fatan zama malami a nan gaba, don horar da kwararrun matasa masu fasaha.

Gasar da ake yiwa taken "Olympics for technicians" a duniya, gasar kwararru ta duniya, gasa ce dake yayata kwarewar sana’a a fannin fasaha. (Ibrahim)