Qatar 2022: Messi ya ceci Argentina kuma Mbappe ya taimaki Faransa shiga kungiyoyin 16 da za su buga zagaye na 2
2022-11-27 17:24:52 CMG Hausa
Yayin da ake ci gaba da buga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya yanzu haka a kasar Qatar, tauraron dan kwallon Argentina Lionel Messi, ya ci wa kungiyarsa kwallo daya, a wasan da ta doke Mexico da ci 2 da nema. Kaza lika a daya wasan da aka buga jiya Asabar, Kylian Mbappe ya ci kwallaye biyu, a wasan da Faransa ta buga da Denmark, inda aka tashi Faransa na da kwallo 2 Denmark na da 1. Da wannan sakamako, Faransa ta samu gurbin buga zagaye na biyu na gasar mai kunshe da kungiyoyi 16.
Har ila yau a dai jiyan, Poland ta doke Saudiyya da ci 2 da nema.
A daya wasan kuma tsakanin Australia da Tunisia, Australia ce ta yi nasara da ci 1 da nema, kuma da wannan sakamako, Australia za ta buga wasan ta na gaba da Denmark. (Saminu Alhassan)