logo

HAUSA

Zamanintar Da Sha’Anin Gona Da Kauyuka Ya Dogaro Da Halin Da Ake Ciki Da Muradun Jama’A

2022-11-27 21:22:03 CMG HAUSA

Daga MINA

Abokai, yawan gonakin Sin da ake iya shuka amfanin gona kaso 9% kawai na dukkan gonakin duniya, amma Sin ta ciyar da dukkan al’ummar Sinawa da yawansu ya kai kashi 20% na al’ummar duniya da wadannan gonaki. Alkaluma na nuna cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, kasar Sin za ta iya samar da kashi 88% na yawan hatsin da al’ummar Sinawa ke bukata da kanta. Ba ma kawai Sin ta warware batun samar da isashen hatsi ga al’ummarta dogaro da karfin kanta ba, har ma ta gudanar da nagartattun tsare-tsaren kawar da talauci bisa halin da take ciki, ya zuwa karshen shekarar 2020, an kawar da talauci a duk fadin kasar, kafin shekaru 10 da MDD ta tsara. Gudunmawar kashi 70% da kasar Sin ta bayar a bangaren kawar da talauci, ya sa Sin ta tabbatar da wadatar al’ummar Sinawa, matakin da ya sanya ta shiga sabuwar hanyar zamanintar da sha’anin gona da raya kauyuka. Yau “Duniya a zanen MINA” zai gabatar muku yadda Sin ta gabatar da wannan buri.

Kasar Sin ta samarwa jama’arta isashen hatsi da kawar da talauci da tabbatar da zaman wadatar al’ummarta da bunkasa kauyukanta duk bisa halin da ake ciki da ma fito da tsare-tsare masu hangen nesa. A karkashin jagorancin gwamnatin Sin, an fitar da wata sabuwar hanya dogaro da kanta ta zamanintar da sha’anin gona da raya kauyuka da wadatar da manoma bisa halin da ake ciki da bukatun al’umma.

Ko shakka babu, wannan sabuwar hanyar da Sin take bi, zai ba da gudunmawa da wayin kai irin na kasar Sin wajen daidaita matsalar karancin abinci da gaggauta bunkasuwar sha’anin gona a duniya, har ma zai karawa duniya musamman ma kasashe masu tasowa kwarin gwiwa wajen samun bunkasuwa mai kyau. (Mai zane kuma mai rubuta: MINA)