logo

HAUSA

An gudanar da tseren yada-kanin-wani karo na 5 a Libya

2022-11-27 17:30:54 CMG Hausa


A jiya Asabar ne aka gudanar da gasar tseren yada-kanin-wani da ake shiryawa duk shekara a kasar Libya. Gasar ta bana dai na da taken "Fafatawa domin zaman lafiya", ta kuma hallara masu tsere sama da 1,500 daga kasashen Libya, da Tunisia, da Aljeriya, da Morocco, da Najeriya, da Türkiyya, da Philippine da Japan.

A cewar shugaban kwamitin tsara gasar da ta gudana a birnin Tirabulus Abdul-Hamed Shbet, baya ga masu tsere, akwai kuma masu sanya ido da alkalai 70, da suka ganewa idanun su yadda ta wakana.

Yayin gasar ta gudun kilomita 21, wato kusan rabin tsayin makamanciyarta da ake yi yayin gasannin kasa da kasa, an shafe kimanin tsawon sa’o’i 3 kafin kaiwa layin karshe. Kuma dan wasan tsere da ya zo matsayi na farko, ya samu kyautar kudin kasar ta Libya dinar 5,500, kwatankwacin dalar Amurka 1,119, da kuma tikitin komawa gida kasar Türkiyya.   (Saminu Alhassan)