logo

HAUSA

Abokai na zahiri suna zurfafa huldar zumunci a sabon zamani

2022-11-26 16:15:57 CMG Hausa

Jiya Jumma’a ne babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Cuba Miguel Díaz-Canel wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin, inda suka amince cewa, za su ci gaba da kara karfafa jagorancin siyasa kan huldar jam’iyyunsu da ma kasashe biyu, tare kuma da ci gaba da kara zurfafa huldar zumunci ta musamman dake tsakanin Sin da Cuba a sabon zamanin da ake ciki.

Duk da cewa, kasashen biyu na da nisa a tsakaninsu, amma huldar dake tsakaninsu tana da kyau kwarai, kuma Díaz-Canel, shi ne shugaba na farko daga nahiyar Latin Amurka da ya kawo ziyara kasar Sin, bayan babban taron wakilan JKS karo na 20, lamarin da ya nuna cewa, huldar dake tsakanin Sin da Cuba ta kasance abin koyi ga kasashe masu bin tsarin gurguzu da kasashe masu tasowa yayin da suke kokarin taimakawa juna.

Yayin tattaunawar ta su, shugaba Xi ya waiwayi zumuncin dake tsakanin Sin da Cuba, shugaba Díaz-Canel shi ma ya bayyana cewa, kasarsa tana mai da hankali matuka kan huldarta da kasar Sin, duk wadannan sun nuna cewa, sassan biyu suna darajanta dadadden zumuncin dake tsakaninsu.

Ko shakka babu ziyarar shugaban kolin Cuba a kasar Sin, za ta kara habaka hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. (Jamila)