logo

HAUSA

An kulle wuraren dake kusa da sansanin sojojin Sao Tome and Principe da aka kai hari

2022-11-26 16:22:37 CMG Hausa

 Da asubahin jiya ne, aka ji karar harbe-harbe a sansanin sojojin fadar mulkin kasar Sao Tome and Principe. Wakilin CMG ya ba da labari cewa, yanzu an kulle wuraren dake kusa da sansanin, ‘yan sandan kasar sun dauki tsauraran matakai domin tabbatar da tsaro a birnin.

Gwamnatin kasar Sao Tome and Principe ta fitar da wani rahoto jiya cewa, jiya da tsakar rana da misalin minti 40, wasu sojoji hudu wadanda suka yi ritaya sun kutsa kai cikin sansanin, inda suka tsare wasu sojoji, suka kuma nemi kwace makaman dake sansanin, a sa’i daya kuma, wasu dakaru masu dauke da matakai da ba a san ko su waye ba, dake wajen sansanin sun taimaka musu, daga baya sassan biyu sun yi musanyar wuta mai tsanani, har zuwa karfe 6 na safe, a sanadin haka, mutane da dama sun rasa rayuka ko jikkata.

Gwamnatin kasar ta bayyana lamarin a matsayin juyin mulkin da bai yi nasara ba, kuma yanzu al’amura sun daidai a kasar, haka kuma gwamnati ta yi kira ga al’ummar kasar da sauran kasahen duniya da su kwantar da hankalinsu. (Jamila)