logo

HAUSA

Sin tana bayar da damar hadin gwiwa ta hanyar ayyukan binciken duniyar wata na Chang’e

2022-11-25 19:39:09 CMG Hausa

Hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin (CNSA) ta bayyana yawan na’urorin nazarin kimiyya da kasashen duniya za su ajiye, wajen gudanar da aikin binciken duniyar wata na Chang’e-6 tare da sanar da wani kira ga kasa da kasa, na shawarar ajiye na’urorin game da shirin binciken na Chang’e-7.

Hukumar ta sanar da cewa, za ta dauki na’urorin kimiyya daga kasashen Faransa da Italiya da hukumar kula da sararin samaniya ta Turai/Sweden a na’urar Chang’e-6 da kuma wani nau’ na kayan aikin Pakista a kan na’urar da za a harba. (Ibrahim)