Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane a kalla 60 a jihar Zamfara
2022-11-25 14:25:38 CMG Hausa
Rahotanni daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya na cewa, masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane a kalla 60 a jihar, lokacin da suke halartar taron Mauludi.
Shaidu daga yankin sun tabbatar da aukuwar al’amarin a jiya Alhamis, a wani yanayi mai muni, na sake yin garkuwa da mutane da jihar ta jima tana fama da shi. (Saminu Alhassan)