logo

HAUSA

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa na kasar Cuba

2022-11-25 14:14:21 CMG HAUSA

Da safiyar yau Jumma’a 25 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Cuba Miguel Diaz-Canel, wanda shi ne sakatare na farko na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Cuba, wanda kuma a yanzu haka yake ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin.

A yayin shawarwarin, Xi ya ce, kasar Cuba, ita ce kasa ta farko da ta kulla huldar diplomasiyya a tsakaninta da jamhuriyar jama’ar kasar Sin a bangaren yammacin duniya. Kuma huldar da ke tsakanin Sin da Cuba, ta zama abun misali a fannin hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen gurguzu, da kuma taimakawa juna a tsakanin kasashe masu tasowa cikin sahihanci.

Ya ce kasar Sin na son kara zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa a tsakaninta da Cuba, da habaka hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin kasashen 2, da mara wa juna baya kan batutuwan da suke shafar babbar moriyar juna, da taimakawa juna a al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da raya kasa ta gurguzu mai halin musamman kafada da kafada, da kuma zurfafa huldar da ke yi tsakanin Sin da Cuba a sabon zamani.

A nasa bangaren, Miguel Diaz-Canel ya ce, ziyararsa ta nuna yadda Cuba ke dora muhimmanci kan raya huldar hadin gwiwa a tsakaninta da Sin. Kaza lika Cuba ta amince da yadda kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karkashin shugabancin Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar, ya ba da gudummowa a tunani da aiki, a fannin raya kasar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin a sabon zamani, lamarin da a ganin Cuba, ya karfafa gwiwar dukkan sassan duniya masu kokarin samun ci gaba sosai. (Tasallah Yuan)