logo

HAUSA

Taiwan Bangare Ne Da Ba Za A Iya Raba Shi Da Kasar Sin Ba

2022-11-25 14:17:17 CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya bayyana cewa Taiwan, bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin. Kaza lika duk wani yunkuri da ake yi na inganta huldar aikin soja a tsakanin Taiwan da kasar Amurka ba zai yi nasara ba.

Wu Qian ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, a lokacin da ya amsa tambayar da aka yi masa, dangane da batu mai nasaba da Taiwan, cikin kwamitin kimanta harkokin tattalin arziki da tsaro tsakanin Amurka da Sin karkashin shugabancin majalisar dokokin Amurka.

Kakakin ya kara da cewa, yayin da shugabannin Sin da Amurka suka gana da juna a ranar 14 ga wata, shugaba Joe Biden ya sake jaddada rashin goyon bayan samun ‘yancin kan Taiwan, da kasancewar “Sin guda 2 a duniya”, ko kuma kasancewar “kasar Sin da kasar Taiwan a dunkule”. Ya ce Amurka ba ta da niyyar ta da hargitsi da kasar Sin. Kuma kasar Sin na fatan Amurka za ta aiwatar da abun da shugaba Biden ya fada, za ta mutunta ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da tanade-tanaden da ke cikin sanarwoyin hadin gwiwa guda 3 a tsakanin Sin da Amurka, ta yadda ba za a kara lahanta moriyar bai daya ta kasashen 2 ba. (Tasallah Yuan)