logo

HAUSA

Shugaban UNECA ya yi kira da a kara azama wajen bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afirka

2022-11-25 10:47:44 CMG Hausa

Mukaddashin babban sakataren hukumar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta MDD ko UNECA Antonio Pedro, ya jaddada bukatar zurfafa hada-hadar cinikayya tsakanin kasashen Afirka, ta yadda hulda tsakanin kasashen za ta iya jure duk wani kalubale daka iya bullowa daga waje.

Pedro wanda ya yi wannan kira a ranar Laraba, ya ce idan har kasashen Afirka suka kara fadada cinikayya tsakaninsu a fannoni mabanbanta, hakan zai baiwa nahiyar damar gina juriyar nahiyar, ta yadda za ta iya jure duk wani yanayi daka iya girgiza tattalin arzikin nahiyar daga ketare.

Jagoran na UNECA ya yi wannan tsokaci ne yayin taron hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka AU, wanda ya gudana a wani bangare na babban taron tattauna batutuwan da suka shafi bunkasa masana’antun nahiyar, da raya tattalin arziki, da kuma taron musamman na AU game da yarjejeniyar yankin ciniki maras shinge na Afirka ko AfCFTA, wanda aka tsara gudanarwa tsakanin ranakun 20 zuwa 25 ga watan nan na Nuwamba a birnin Yamai, fadar mulkin jamhuriyar Nijar.

Pedro ya kara da cewa, nahiyar Afirka ta sha fama da tasirin annobar COVID-19 sama da wasu yankunan duniya, da tasirin rikicin Ukraine, saboda yawan dogaron ta ga hajojin da ake shigowa da su daga waje.

Daga nan sai ya jaddada wanzar da ci gaban tattalin arzikin Afirka a matsayin hanya mafi dacewa, ta ingiza wanzuwar bunkasar masana’antun Afirka.

Kaza lika Pedro ya ja hankalin kasashen Afirka, game da muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar ciniki maras shinge, a matsayin makamin ingiza sauyi a Afirka, wanda zai karfafa cinikayya da raya masana’antun nahiyar.   (Saminu Alhassan)