logo

HAUSA

Qatar 2022: Japan ta doke Jamus da ci 2 da 1

2022-11-24 11:44:30 CMG Hausa

 

A ci gaba da buga wasannin cin kofin kwallon kafar duniya da ake yi a Qatar, a wasan rukunin E na jiya Laraba, Japan ta yi nasara kan Jamus da ci 2 da 1, duk da cewa a tarihin gasar, Jamus ta dauki kofin har karo 4.

Wasan na jiya ya ba da mamaki matuka, kamar dai yadda ta kaya tsakanin Saudiyya da Argentina a ranar Talata, inda Saudiyyar ta doke Argentina da ci 2 da 1.

Bisa sakamakon wasan na jiya, Jamus ta shiga tsaka mai wuya, duba da cewa a wasannin da suka rage mata na rukunin E, za ta fafata ne da Sifaniya da kuma Costa Rica, bayan kungiyoyin biyu sun barje gumi tsakaninsu a Larabar nan.   (Saminu Alhassan)