logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya kaddamar da kudin kasar da aka sauyawa fasali

2022-11-24 11:41:20 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da takardun kudin kasar da aka sauyawa fasali a jiya Laraba, a wani mataki na inganta zagayawar kudaden kasar.

Cikin jawabin da ya gabatar a birnin Abuja yayin kaddamar da sabbin takardun kudaden na Naira 200, da 500, da 1000, shugaba Buhari ya yi cikakken bayani game da dalilan da suka sa ya amince babban bankin kasar ya gudanar da sauyin. Yana mai cewa, sabbin takardun kudaden na dauke da alamomi na tsaro da za su dakile yunkurin masu son buga na jabu.

Ya ce, "Akwai matukar bukatar shawo kan matsalar boye takardun kudin kasar da wasu ke yi maimakon ajiya a banki, wanda hakan ke haifar da karancin kudade a hannun jama’a, kana akwai karancin takardun kudi masu tsafta dake kewayawa tsakanin al’umma, kana an samu karuwar kudaden jabu na manyan takardun kudin kasar. Hakan ne ya sa gwamnati ta amince da sauya fasalin Naira 200, da 500, da 1,000, bayan da a farkon shekarar nan babban bankin kasar CBN, ya nemi amincewar shugaban kasar game da hakan”. (Saminu Alhassan)