logo

HAUSA

An gano sabon filin iskar gas a kudu maso yammacin Sin

2022-11-24 20:47:59 CMG Hausa

Kamfanin mai na Sinopec, dake zama kamfanin tace mai mafi girma a kasar Sin, ya gano wani sabon fili na iskar gas, wanda aka yi amannar ya kai kusan cubic mita biliyan 146, a tabkin Sichuan dake yankin kudu maso yammacin kasar Sin.

Shugaban kamfanin Sinopec Ma Yongsheng, ya bayyana cewa, sabon filin iskar gas din, yana cikin yankin Qijiang na birnin Chongqing da gundumar Xishui ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin.(Ibrahim)