logo

HAUSA

Sin za ta aiwatar da manufofin tallafawa farfadowar tattalin arziki

2022-11-24 11:42:44 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, Sin za ta aiwatar da kwararan matakai na tabbatar da an aiwatar da cikakkun manufofin samar da daidaito, da sanya ido kan tattalin arzikin kasar, a wani mataki na karfafa ginshikin farfadowa da bunkasarsa.

Li Keqiang ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin taron majalissar zartaswa da ya jagoranta. Yayin taron, an kuma amince da kara tallafi ga sassa masu zaman kansu, a fannin bayar da takardun lamuni, da amfani da manufofin hada hadar kudade wajen kiyaye ka’idojin raba riba a duk lokacin da aka bukaci hakan, domin tabbatar da kare kimar kadarori bisa doka. (Saminu Alhassan)