logo

HAUSA

Sharhi:Yaushe ne za a ga bayan hare-haren bindiga a kasar Amurka?

2022-11-24 22:02:58 CMG Hausa

Yayin da ake dab da fara bikin gargajiya a kasar Amurka wato ThanksGiving Day, an sake samun harbe-harben bindiga a kasar. A ranar 22 ga wata, agogon wurin, harin bindiga da ya auku a wani kantin zamani da ke birnin Chesapeake na jihar Virginia, ya yi sanadin mutuwar mutane shida, tare da jikkatar wasu hudu. Kwanaki uku kafin wannan hari, wani harin bindiga da ya auku a birnin Springs na jihar Colorado ya halaka mutane biyar, tare da jikkata wasu 25.

Ranar ThanksGiving biki ne na haduwar iyali, amma hakan ba zai yiwu ba ga iyalai da dama sakamakon hare-haren bindigar dake faruwa.

Ba da jimawa ba ne, wani hoton bidiyo ya karade shafin yanar gizo, inda ake ganin wata ’yar Amurka ta saya wa danta mai shekaru 5 da haihuwa wata jakar makaranta da za ta iya kare shi daga harbin bindiga, tare da horar da shi a gida kan yadda zai iya gudu daga hare-haren bindiga. Wadanda suka kalli bidiyon da dama sun ce, hakan abin bakin ciki ne. Babu shakka, sai dai gaskiyar lamarin da ya faru ya fi hakan bakin ciki, idan ba a manta ba, a ranar 24 ga watan Mayun bana, harin bindiga da ya faru a makarantar firamare ta Robb, ya yi sanadin mutuwar yara 19 da ma malamai 2, lamarin da ya jawo suka daga bangarori daban daban kan rashin daukar matakan shawo kan matsalar da gwamnati ta yi.

Alkaluman da shafin yanar gizo dake bayani game da matsalar harbin bindiga mai suna “Gun Violence Archive” ya fitar, sun yi nuni da cewa, tun farkon bana har zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba, mutane sama da dubu 39 sun mutu sakamakon hare-haren bindiga a kasar ta Amurka, kuma shekaru uku a jere yawan harbe-harben bindiga da suka faru a duk shekara ya wuce 600 a kasar.

Yara manyan gobe, abin kunya ne yadda kasar ta Amurka ta kasa kare yaranta daga hare-haren bindiga. Rayuka su ne tushen hakkin dan Adam, kuma abin takaici ne yadda hare-haren bindiga suke ta halaka ’yan kasar. (Mai Zane: Mustapha Bulama)