logo

HAUSA

Gudummawar Kamfanonin Fasahar Sadarwar Kasar Sin Ga Kara Dunkulewar Duniya

2022-11-24 19:26:57 CMG HAUSA

DAGA Saminu Hassan

A wannan lokaci da muke cikin yanayi na dunkulewar al’ummun duniya wuri guda, hidimomin sadarwa na da matukar muhimmanci, kasancewar suna bude karin kofofin raya tattalin arziki, da kyautata zamantakewar al’ummu daban daban. Kaza lika damar sadarwa tsakanin al’ummun duniya ta riga ta zama daya daga cikin hidimomi masu daraja na more rayuwar bil adama.

Hakan ne ma ya sa karkashin kyawawan manufofin kasar Sin, gwamnati ke karfafa gwiwar sassa daban daban, musamman kamfanonin kasar da su tallafa, wajen bunkasa samar da ababen more rayuwa ga al’ummun duniya a duk inda suke.

A baya bayan nan, kamfanin ayyukan fasahar sadarwa na kasar Sin wato Huawei, ya alkawarta hade sassan al’ummun duniya miliyan 120, dake rayuwa a wurare masu wuyar kai wa, a kasashen duniya da yankuna sama da 80 da layukan sadarwar wayar tafi-da-gidanka, nan zuwa karshen shekarar 2025.

Fatan kamfanin shi ne kara fadada gajiyar sadarwar wayar hannu ga al’ummun duniya, ta yadda za su ci riba daga fasahohin bunkasa tattalin arziki, da kasuwanci, da inganta sha’anin zamantakewa, da dasa tunani mai kyau a fuskar samar da ci gaba mai dorewa.

Dama dai ya zuwa karshen shekarar 2021, kamfanin na Huawei, karkashin shirinsa na “RuralStar telecom solutions”, wato shirin samar da turakun sadarwar salula a kauyuka, ya rika ya hada sama da mutum miliyan 60 dake rayuwa a wurare masu wuyar shiga, a kasashe da yankunan duniya sama da 70 da layukan wayar hannu.

Ba shakka irin wannan tunani, na fadada damar al’ummun yankunan karkara, da mutanen dake zaune a wurare masu nisa, na samun hidimomin wayar sadarwa da kamfanin Huawei ke aiwatarwa abun a yaba ne. Kuma wata muhimmiyar hanya ce da kamfanonin Sin ke bi wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin al’ummun duniya, musamman al’ummun kasashe masu tasowa. (Saminu Hassan)