logo

HAUSA

Shugaban Laos zai ziyarci kasar Sin

2022-11-24 15:29:13 CMG Hausa

 

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar juyin juya hali ta Laos, kana shugaban kasar Thongloun Sisoulith, zai yi ziyarar aiki a kasar Sin tsakanin ranakun 29 ga watan Nuwambar nan zuwa 1 ga watan Disamba dake tafe, bisa gayyatar da babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa.

A yau Alhamis ne kakakin sashen lura da al’amuran kasa da kasa na kwamitin kolin JKS Hu Zhaoming ya tabbatar da hakan. (Saminu Alhassan)