logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da hoton rana da aka dauka da HXI irinsa na farko

2022-11-24 19:53:22 CMG Hausa

Kasar Sin ta fitar da wani hoton saman rana bisa kimiya a ranar Litinin, hoto na farko da ta dauka da na’urar HXI a sararin samaniya, kuma irinsa daya tak da ake da shi a duniya.

Tashar sanya ido kan harkokin sararin samaniya dake kan tsaunin Zijin na cibiyar kimiya ta kasar Sin (CAS) ce ta fitar da wannan hoto, wanda tauraron dan-Adam na Kuafu-1 na kasar Sin da na’urar sanya ido kan harkokin sararin samaniya (ASO-S) suka dauka, aka kuma yi nasarar harba ta daga cibiyar harba taurarin dan-Adan ta Jiuquan a watan Oktoba.(Ibrahim)