logo

HAUSA

Kudin Da Sana’Ar Kere-Keren Kasar Sin Ya Jawo Daga Waje Ya Kara Karuwa

2022-11-24 19:31:45 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

Yau Alhamis, ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta shirya taron manema labarai, inda kakakinta Shu Jueting ta nuna cewa, a bana yawan kudaden da sana’ar kere-keren kasar ya jawo daga waje ya karu matuka.

A cewarta, kamfanonin kasa da kasa da dama sun kara zuba jari a kasar Sin saboda boyayyen karfin kasuwannin Sin da cikakken tsarin masana’antu da ingantuwar manyan ababen more rayuwa da yanayin al’umma mai dorewa. Hakan ya sa, ake gaggauta kafa wasu manyan ayyuka dangane da sana’ar kere-kere. Ya zuwa shekarar 2021, yawan kudaden wajen da Sin ta shigo da su a wannan fanni ya kai dala biliyan 33.73, wanda ya karu da kashi 8.8% bisa na makamancin lokaci na 2020.(Amina Xu)