logo

HAUSA

An kaddamar da taron kasa da kasa game da sarrafa hajoji masu amfani da fasahohin AI

2022-11-24 11:40:51 CMG Hausa

A kaddamar da taron kasa da kasa game da sarrafa hajoji masu amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, wato AI a birnin Nanjing, hedkwatar lardin Jiangsu na kasar Sin a jiya Laraba. Taron zai mai da hankali kan abubuwan dake jawo hankalin masu ayyukan sarrafa hajoji, ta yin amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, tare da yin musayar ra’ayoyi a tsakaninsu, don gano hanyar yin kirkire-kirkire da kuma samun karin ci gaba a wannan fanni.

Mataimakin minista mai kula da masana’antu da sadarwa na kasar Sin Mista Xin Guobin, ya bayyana a gun taron cewa, ayyukan sarrafa hajoji masu amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, suna haifar da manyan sauye-sauye ga hanyoyin aiki da ma rayuwar dan Adam, kuma bunkasa ayyukan ya zama wani zabi na bai daya ga kasa da kasa. Yana mai cewa,“Kasar Sin tana da kasuwa mafi girma ta sarrafa hajoji masu amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama a duniya, kuma tana son hada hannun kasa da kasa, don inganta huldar abokantaka ta fannin bunkasa ayyukan sarrafa hajoji masu amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, tare da samar da gudummawar kasar Sin ga ci gaban ayyukan a duniya.”  (Lubabatu)