logo

HAUSA

Kasashen Turai Sun Fusata Da Matakin Amurka

2022-11-24 11:55:44 CMG HAUSA

A daren ranar 21 ga wata, a fadar shugaban kasar Faransa ta “Elysee”, shugaba Emmanuel Macron na kasar ya shirya wata liyafa, inda ‘yan kasuwar kasashen Turai da dama suka halarta, ciki hadda manyan jami’an kamfanonin Ericsson, da Volvo, da Unilever. Mr. Macron ya shirya liyafar ba domin murnar wani abu ba, sai don fatan wadannan kamfanoni ba za su bar kasashen Turai su je kasar Amurka ba.

Yanzu farashin makamashi ya karu matuka a kasashen Turai, wanda hakan ya sa kudin sarrafa hajoji ya karu sosai, lamarin da ya sanya kamfanonin kasashen Turai fuskantar matsananciyar matsala. Kamar yadda wani babban jami’in kawancen masana’antun sarrafa karfe na kasar Faransa ya fada, kila matsakaicin farashin iskar gas da wutar lantarki zai karu da ninki 4. Amma a kasar Amurka, farashin makamashi bai sauya da yawa ba, kana kuma, shirin dokar yaki da hauhawar farashin kaya da gwamnatin kasar Amurka ta zartas, ya samar wa kamfanonin da ke Amurka kudin alawas da yawa, shi ya sa kamfanonin kasashen Turai ba abun da za su yi, sai dai janyewa daga nahiyar Turai, su koma kasar Amurka.

A watan Agustan bana, gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da shirin dokar yaki da hauhawar farashin kaya, a kokarin samar wa kamfanonin kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Amurka kudin alawas, amma shirin dokar bai shafi kamfanonin kasashen kungiyar EU, Japan, da Koriya ta Kudu ba. Irin wannan shirin doka maras adalci, ta sanya kamfanoni masu ruwa da tsaki juya hankalinsu daga masana’antun kera motoci masu amfani da wutar lantarki na Turai, zuwa kasar Amurka.

Kasashen Turai sun yi matukar fusata da hakan. Har ma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi Amurka da laifin ba da kariya kan cinikayya. Kana ministan tattalin arzikin kasar Jamus Robert Habeck ya ce, Amurka tana cin zalin Turai yanzu. Har ila yau jami’an EU sun zargi Amurka da laifin saba wa ka’idojin kungiyar cinikayyar duniya.

Kaza lika a ranar 22 ga wata, kasashen Faransa da Jamus, sun ba da sanarwar hadin gwiwa, inda suka nuna cewa, za a kiyaye masana’antun Turai da kauracewa shirin dokar Amurka ta yaki da hauhawar farashin kaya cikin hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)