logo

HAUSA

Shugabannin Sin Da Congo(Kinshasa) Sun Aike Wa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 50 Da Dora Huldar Kasashen Biyu Kan Hanyar Da Ta Dace

2022-11-24 15:48:37 CMG HAUSA

Yau Alhamis ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwaransa na kasar Congo(Kinshasa) Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 50 da dora huldar da ke tsakanin kasashen 2 kan hanyar da ta dace.

A cikin sakonsa, Xi ya nuna cewa, a rabin karnin da ya gabata, kasashen 2 sun raya hulda a tsakaninsu yadda ya kamata, sun kuma rika zurfafa dankon zumunci a tsakaninsu. A shekarun baya, kasashen biyu sun kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kuma hadin gwiwarsu ya haifar da sakamako mai yawa, kuma hakan ya amfani al’ummomin kasashen biyu. Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmanci kan raya dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Congo(Kinshasa), yana kuma son yin kokari tare da shugaba Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, wajen yin amfani da damar cika shekaru 50 da dora huldar kasashen biyu a kan hanyar da ta dace, domin zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da inganta hadin gwiwarsu a fannin aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma bude sabon babi na bunkasar huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo ya ce, a cikin shekaru 50 da suka wuce, kasarsa da Sin sun bunkasa hulda a tsakaninsu yadda ya kamata ba tare da kasala ba. Yana kuma fatan kara zurfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu, da kara azama kan samun sabbin sakamako wajen bunkasar huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, a kokarin kawo wa jama’ar kasashen biyu alheri. (Tasallah Yuan)