logo

HAUSA

An Bude Bikin Anime Na Kasa Da Kasa Karo Na 18 A Hangzhou

2022-11-24 11:57:55 CMG HAUSA

Yau Alhamis ne aka bude bikin anime na kasa da kasa karo na 18 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin. Babban taken shagalin shi ne “Samun wadata tare a sabon zamani, da kuma samun kyakkyawar makoma a fannin anime”. Za a nuna sabbin nasarorin da masana’antun anime na kasar Sin suka samu, da ci gaban masana’antun da kuma makomar su a gun bikin. (Tasallah Yuan)