logo

HAUSA

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Nijeriya

2022-11-23 10:19:05 CMG Hausa

 

Jimilar mutane 37 ne suka mutu, sanadiyyar taho-mugama da wasu motocin safa biyu suka yi jiya Talata, a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Kwamandan hukumar kiyaye aukuwar haddura a jihar Borno Utten Boyi, ya shaidawa manema labarai cewa, motocin biyu sun kama da wuta bayan taho-mugamar a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Jami’in ya ce za a binne mutanen baki daya a yau Laraba, yana mai cewa ‘yan sanda sun riga sun samu amincewar kotu game da hakan.

A wani labarin kuma, mutane 17 sun mutu, yayin da wasu 4 suka jikkata sanadiyyar wani mummunan hatsarin mota da safiyar jiya Lalata, a wajen Abuja, babban birnin kasar.

Kakakin hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasar Bisi Kazeem, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, hatsarin ya auku ne tsakanin wata babbar mota da motar safa, a kan babban titin Kwali zuwa Abaji, a kusa da yankin Awawa. Ya ce bincike ya gano cewa, hatsarin ya auku ne saboda gudun wuce sa’a.

Kakakin ya shawarci direbobi da su rika kiyaye dokokin hanya a ko da yaushe. (Fa’iza Mustapha)