logo

HAUSA

Shugaban kasar Ghana ya alkawarta bunkasa hadin gwiwar dakile bazuwar ta’addanci a yammacin Afirka

2022-11-23 10:17:19 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya alkawarta bunkasa hadin gwiwa da sauran sassan, wajen dakile bazuwar ta’addanci daga yankin Sahel zuwa yankunan yammacin Afirka dake bakin teku.

Shugaba Akufo-Addo ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin kaddamar da taron shugabanni a dandalin Accra, na hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen yammacin Afirka 7 da na yankin Sahel.

Ya ce "Tabarbarewar yanayin tsaro a yankin Sahel, na barazanar hadiye dukkanin yammacin Afirka. Kungiyoyin ta’addanci dake kara kaimi sakamakon nasarori da suke samu a yankin, suna sake gano sabbin dabarun cimma burikansu, lamarin da ke ta’azzara yaduwar ayyukansu daga Sahel zuwa yammacin Afirka”.

Shugaban na Ghana ya kara da cewa, duk da cewa yanzu ne dandalin Accra ke tasowa, karkashinsa an fito da muhimmancin hadin gwiwar gwamnatocin kasashen nahiyar, a fannin karfafa yaki da bazuwar ta’addanci daga Sahel zuwa yammacin Afirka.  (Saminu Alhassan)