logo

HAUSA

An kaddamar da hakar man fetur a yankin arewa maso gabashin Nijeriya a karon farko

2022-11-23 15:48:15 CMG Hausa

 

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da aikin hakar man fetur da iskar gas na Kolmani, a yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar jiya, a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar, Muhammadu Buhari ya ce izinin hakar man fetur mai lamba 809 da 810 na Kolmani dake kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe, ya zama wurin hakar man fetur na farko a arewa maso gabashin Nijeriya, bayan samun adadi mai yawa na danyen mai a yankin, shekaru biyu da suka gabata.

An gano gangar mai sama da biliyan 1 da iskar gas mai yawan cubic meter biliyan 14.2 a wurin.

Shugaban na Nijeriya ya bayyana sabon wurin hakar man a matsayin wani karin muhimmin ginshinkin tattalin arzikin kasar, yana mai jinjina dimbin alfanun da aikin zai kawowa kasar, ciki har da wadatar makamashi da kudin shiga da kuma ci gaban tattalin arziki da zaman takewa. (Fa’iza)