logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin fina-finan Asiya karo na 4 a Najeriya

2022-11-23 11:06:47 CMG Hausa

A ranar Litinin 21 ga watan Nuwambar nan ne aka kaddamar da baje kolin fina-finan Asiya karo na 4 a Najeriya. Bikin wanda ofisoshin jakadancin kasashen Asiya 9 da suka hada da Sin, da Iran da Koriya ta kudu, da kuma Najeriya suka yi hadin gwiwar shiryawa, ya gudana ne a cibiyar nune-nunen al’adun kasar Sin dake birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Cikin jawabinsa yayin bude bikin, jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya ce al’adu su ne ruhin kowace kasa, kuma musayar al’adu tamkar musayar zuciyoyi da rayukan al’ummun kasashen duniya ne. Kaza lika fina-finai na nuna yanayi na sassan al’adun al’ummu daban daban.

Jakada Cui ya ce dandalin baje kolin fina-finai na hadin gwiwar kasashe daban daban, muhimmiyar hanya ce ta gina dandalin fahimtar al’adun juna, da ma yanayin rayuwar al’ummu, kuma hakan zai ci gaba da ba da gudummawa wajen zurfafa fahimtar juna tsakanin al’ummu, da inganta kawancen kasashe.

Ya ce karkashin hakan, za a iya kyautata fahimtar juna, da inganta kawance dake maye gurbin kyamar juna, kana mutane za su kara rayuwa cikin lumana, kuma duniya za ta samu ci gaba cikin yanayin zaman lafiya. Har ila yau, musayar al’adu kyakkyawar manufa ce da duniya ke son cimmawa, kuma hakan shi ne ainihin dalilin shirya bikin na wannan karo.

Daga nan sai jakada Cui ya shawarci mahukuntan Najeriya da su shirya makamancin wannan biki a Sin, domin baiwa Sinawa damar kallon fina finan Najeriya, tare da kara fahimtar kasar, a matsayinta na babbar kasa a nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)