logo

HAUSA

Da Babu Gara Babu Dadi

2022-11-23 16:12:27 CMG HAUSA

A kwanakin baya ne, aka kawo karshen babban taron kasashe masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 27 wato COP27 a wurin shakatawa na Sharm el Sheikh dake kasar Masar, wanda tun farko aka shirya kammala shi a ranar 18 ga wata, inda mahalarta taron suka zartas da kudurori da yawa, tare da yanke shawarar kafa wani asusu na musamman da zai tattara kudaden taimakawa kasashe masu tasowa da wadanda ke fama da matsalar sauyin yanayi.

Taron na bana, shi ne na 27 da kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko UNFCCC suka gudanar, kuma cikin wata sanarwa da ya fitar game da hakan, babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi na’am da kafa asusun, wanda zai samar da diyyar asara da lalacewar muhalli, yana mai fatan asusun zai yi aiki yadda ya kamata. Fata dai shi ne, a gani a kasa, wani ana biki a gidansu kare.

Taron na Sharm El-Sheikh na kasar Masar, ya zamo wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci. Sai dai kuma a cewar Guterres, duk da cewa, kudaden da ake fatan tarawa ba za su isa ba, yunkurin tara kudaden kadai, tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce. Idan ruwanka bai isa alwala ba, aka ce sai ka yi taimama.

Bugu da kari, taron na COP27 ya yi rawar gani, wajen zakulo matakan jure sauyin yanayi, da tattara kudade na diyyar asara da lalacewar muhalli, wadanda su ne manyan abubuwan damuwa ga kasashe masu tasowa. Yayin taron na bana, kasashe masu wadata sun fito da muhimman batutuwa da suka dace, kamar batun samar da kudade, da tallafin kwarewa da kasashe masu tasowa ka iya cin gajiyar su, suna fatan kasashe masu wadata za su yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen gina yanayi mai dorewa domin gobe.

Fata dai shi ne kasashe masu sukuni, za su ba da gudummawar da za ta kai ga cimma nasarar kudurin dake kunshe cikin yarjejeniyar Paris, ta hanyar kafa asusun diyyar asara da lalacewar muhalli, domin taimakawa kasashe masu tasowa, ta yadda za su shawo kan kalubalen sauyin yanayi.

Masu fashin baki na cewa, idan har mafarkin kafa wannan asusu ya tabbata tare da aiwatar da shi kamar yadda aka tsara, to, wata rana batun matsalar sauyin yanayi za ta kasance tarihi. Fata na gari dai aka ce lamiri. (Ibrahim Yaya)