Kasar Sin ta kuduri aniyar amfani da sararin samaniya cikin lumana
2022-11-23 13:52:48 CMG Hausa
Bayanai daga hukumar kula da ayyukan binciken sararin samaniyar kasar Sin (CMSA) na cewa, an yi jigilar kumbon Shenzhou-15 da rokar Long March-2F da za a yi amfani da ita wajen harba kumbon zuwa sararin sama, kuma dukkansu suna cikin yanayi mai kyau. Za kuma a kammala dukkan gwaje-gwajen na’urorin kamar yadda aka tsara.
Wannan wani bangare ne na jerin shirye-shiryen aka tsara cikin jerin matakan ayyukan gina tashar binciken sararin samaniyar kasar cikin nasara. Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne, kasar Sin ta yi nasarar harba dakin gwaje-gwaje na biyu na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya, matakin dake kara kusanto ta ga aikin kammala tashar ya zuwa karshen wannan shekara.
Daga baya, dakin gwajin na Mengtian zai sauya mazauninsa kamar yadda aka tsara. Dakin gwaji na Mengtian, da takwaransa na Wentian da babban bangare na Tianhe ne za su hade su ba da siffar T ta tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin.
Aikin gina tashar ya kasance muhimmin mataki a aikin binciken sararin samaniyar kasar Sin, inda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka wajen raya aikin bisa manufofin amfani da albarkatun sararin samaniya ta hanyar zaman lafiya, da nuna adalci don cimma moriyar juna, da kuma bunkasa harkokin dake da nasaba da hakan cikin hadin gwiwa.
Rahotanni na cewa, a tarihin bil Adama, tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ita ce tasha ta farko da aka bude ga dukkanin mambobin MDD. Kuma yanzu haka, kasar Sin ta bayar da izinin yin gwaje-gwaje a shirye-shirye guda 9 a cikin tashar, ga kasashe guda 17, da kamfanoni guda 23. Lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin ta inganta dunkulewar bil Adama a fannin habaka aikin binciken sararin samaniya.
Bayan an kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin, za a shiga matakin amfani, da kuma raya tashar na tsawon shekaru 10. Ana kuma sa ran nan da kwanaki masu zuwa, kasar Sin za ta harba kumbo mai dauke da ’yan sama jannati na Shenzhou mai lamba 15, ta yadda ’yan sama jannati guda 6 za su yi aiki tare a tashar. Sannan a karshen shekarar da muke ciki, za a kammala aikin gina tashar sararin samaniya ta kasar Sin.
Masu fashin baki na cewa, a nan gaba, tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin za ta kasance “sabon gida a cikin sararin samaniya” ga dukkanin bil Adama, inda za su gudanar da aikin binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa, inda ’yan sama jannati na kasar Sin da na kasashen waje, za su ba da gudummawa ga aikin binciken sararin samaniya, a kokarin karfafa amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)