logo

HAUSA

Manufofin kudi na kasar Sin sun taimakawa habakar tattalin arziki

2022-11-22 14:21:44 CMG Hausa

 

Gwamnan babban bankin kasar Sin Yi Gang, ya ce manufofin kudi da kasar Sin ta dauka, sun bayar da gagagrumin taimako ga tsarin tattalin arzikin kasar, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Yayin taron shekara kan batutuwan hada-hadar kudi na Financial Street Forum na 2022, Yi Gang ya bayyana cewa, yayin da tattalin arzikin kasar ya fuskanci kalubale da matsi a bana, hukumomin hada-hadar kudi na kasar sun dauki manufofin daidaita shi a kan kari, domin kara taimakawa bangaren tattalin arzikin da ya shafi hada-hadar kudi kai tsaye.

Ya ce saboda daidaita manufofin da aka yi a kan lokaci, tattalin arzikin na nan da kwarinsa, kuma farashin kayayyaki na bisa mizani na daidaito duk da hauhawar farashin da ake fuskanta a duniya.

An bude taron wanda ake yi duk shekara ne a jiya Litinin. Wasu na yi masa kallon ma’aunin gyare-gyare da ci gaban bangaren hada-hadar kudi na kasar Sin. (Fa’iza Mustapha),